Module 2-IRE-IREN MOTSI NA ASALI (Types of Motion)

Hausa Language English Language

1. Motsi na barkatai: A wannan irin motsi, abubuwa na tafiya ta hanyar barkatai ko kuma basa bin ka’idar tafiya. Mialin wannan motsin shi ake kira Motsi Brownian. Shi ne motsi na babarkatai daya hada da na iska, ko na hayaki, da dai sauransu.

2. Motsi na mikakken hanya ko layi: Wannan irin motsin, yayi tarayya da motsi a mikakkiyan hanya. Misalan abubuwa dake yin mikakken motsi sun hada da, Tafiyan Nokiliya, tafiyan harsashi, tafiyan Jirgin sama, gudu a mikakken hanya, tafiya mota daga wani guri zuwa wani guri a mikakken hanya, da dai sauransu.

3.Motsi na ajuyawa, ko na kewaya, ko na zagaye: Wannan irin motsi ya hada motsin abubuwa nã kewayawa a tsakiyan guri ko abu. Misali, motsin duniya (kewayar falaki), tafiyan wata nã kewayan duniya, tafiyan gargaren mota, Juyawan kara funan fanka, da dai sauransu.

4. Motsi na kayadadden lokaci: Wannan shi ne tafiya dake da kayadadden lokaci da yake faruwa. Wannan irin motsi yana mai-maita kansa bayan wani lokaci kayadadde. Misalai sun hada da; Tafiyan hannayen agogo, girgizan zaren tambari, kewayen duniya a tsakiyan sa.

1.Random Motion: In this types of motion objects move irregularly or random or haphazardly or disorderly with no preferred direction or orientation. As a result of such random movement the particles collide with one another. An example of such motion is an irregular motion ofparticles of various kinds suspended in water, or of smoke particles suspended in air or motion of gas particles.

2.Translational Motion: This type of motion occurs when an object moves in a fixed direction. When a body moves from one point, for example, point A to another point called B. when rigid body move from one point in space to another without rotating, the motion is said to be translational.

3.Rotational Motion: This is the movement of a body in a rotational manner about its axis. It involves motion of a body in a circle about an axis. Examples, rotation of the earth about its axis, rotation of an electric fan blades, the wheel of a moving car.

4.Periodic, oscillatory or vibratory motion: Periodic motion is a type of motion that occurs very frequently in the motion of a body in a circular path with uniform speed such as the oscillation of a clock pendulum. Examples of such motion are; the balance wheel of watch, the vibration of a violin string and the rotation of the earth about its axes.

 

 

Web-based Physics Lessons in Hausa

Powered by Samterch IT Solutions